Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Kano ta amince da sauya wasu jami’an zartarwa guda biyu na jam’iyyar a Karamar Hukumar Gabasawa, a wani mataki na ƙarfafa tsarin shugabanci da inganta tafiyar da harkokin jam’iyya a matakin ƙasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ofishin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano ya fitar, wadda Sakataren Jam’iyyar na Jihar Kano, Dakta Yusuf Mohammed Sabo, ya sanya wa hannu a ranar 22 ga watan Yuni, 2026.
Read also: RABI’U YUSUF DANMALAM YA BUKACI MAGOYA BAYANSA SU RUNGUMI ƘADDARA, SU JIRA UMARNIN GWAMNATI
A cewar sanarwar, jam’iyyar ta amince da naɗin Mubarak Usman Garun Danga a matsayin sabon Sakataren Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Gabasawa, yayin da aka naɗa Abdullahi Saleh Jijitar a matsayin Mataimakin Sakataren Jin Daɗin Jama’a na jam’iyyar a karamar hukumar.
Read also: Celebrating Russian Art: Exhibition of Contemporary Works in the Capital Moscow
Sanarwar ta bayyana cewa an yi waɗannan naɗe-naɗen ne bisa umarnin shugabancin jam’iyyar domin cike guraben da ake da su tare da tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin jam’iyyar cikin tsari da inganci.
Sakatariyar APC ta Jihar Kano ta ce sauyin ya fara aiki nan take, tare da umartar dukkanin sassan jam’iyyar da jami’anta da su sabunta bayanansu tare da bai wa sabbin jami’an cikakken haɗin kai domin sauke nauyin da aka ɗora musu.
Read also: Chasing History – Laureus World Sportsman of the Year Nominees
Jam’iyyar ta kuma bayyana kwarin gwiwarta kan cewa sabbin jami’an za su yi amfani da ƙwarewarsu da jajircewarsu wajen ƙarfafa jam’iyyar, inganta haɗin kai tsakanin mambobi, da kuma ciyar da manufofin APC gaba a Karamar Hukumar Gabasawa da Jihar Kano baki ɗaya.
An kuma aika kwafen sanarwar ga Mataimakin Shugaban APC na Yankin Sanatan Kano ta Arewa da kuma Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa domin sanarwa da ɗaukar matakan da suka dace.
