Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙananan sauye-sauyen da aka yi a cikin Majalisar Zartarwar Tarayya (FEC).
A cewar wata takarda da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya sanya hannu a kai, an sauke wasu ministoci biyu daga muƙamansu, wato Mista Wale Edun da Injiniya Ahmed Musa Dangiwa.
Read also: Fatima Ameneef na Maraba da Uwargidan Shugaban Kasa Zuwa Kano
Edun, wanda shi ne Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki na Ƙasa, an umarce shi ya miƙa aiki ga Mista Taiwo Oyedele, wanda yanzu zai karɓi muƙamin Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki na Ƙasa. Oyedele ya taɓa zama Karamin Minista a wannan ma’aikata.
Haka kuma, an naɗa Mista Muttaqha Rabe Darma (PhD) a matsayin wanda aka zaɓa kuma Ministan Ma’aikatar Gidaje da Ci gaban Birane.
A nasa ɓangaren, an umarci Dangiwa da ya miƙa aiki ga Karamin Ministan da ke cikin ma’aikatar.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Bukaci Limamai Su Wayar da Kan Al’umma Kan Rijistar Katin Zabe
Takardar ta bayyana cewa dole ne dukkanin miƙa-mikon aiki da karɓa su kammala kafin ƙarshen ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.
Da yake bayani kan wannan mataki, Akume ya ce sauye-sauyen na da nufin ƙara haɗin kai da inganta aiki cikin gwamnati, domin cimma manufofin “Renewed Hope Agenda” na shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi a ƙarƙashin sassa na 147 da 148 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka gyara).
Read also: Sanata Oluremi Tinubu Ta Kaddamar da Titin Lodge, Ta Kuma Kaddamar da Aikin Titin Sarkin Yaki
Shugaban ya kuma gode wa ministocin da suka sauka bisa gudunmawar da suka bayar ga ƙasa, tare da yi musu fatan alheri a gaba.
A ƙarshe, shugaban ya tabbatar wa dukkanin ministoci cewa za a ci gaba da yin gyare-gyare domin ƙarfafa gwamnati.
