Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a harin da ’yan daba suka kai kasuwar sayar da wayoyi ta Farm Centre, bayan rikicin da ya barke a unguwar Gyadi-Gyadi a ranar Litinin.
Jaridar Harcode Online News ta rawaito cewa, wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Litinin 27 ga Afrilu, 2026.
Read also: Jam’iyyar APC a Kano Ta Sauya Wasu Jami’an Jam’iyya a Karamar Hukumar Gabasawa
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 1:20 na rana, inda aka sanar da cewa wasu da ake zargin ’yan daba sun taru domin tada rikici a Gyadi-Gyadi.
Read also: Gwamna Abba ya miƙa sunan Murtala Garo ga Majalisar Kano a matsayin Mataimakin Gwamna
Da isar jami’an sintiri wurin, sun tarar da tarzoma na gudana, inda har aka lalata motar daukar marasa lafiya, tare da yunƙurin kai hari wasu wurare.
Daga bisani, wadanda ake zargin sun tsere zuwa kasuwar Farm Centre, inda suka yi yunƙurin shiga shaguna domin wawashe kaya. Sai dai rundunar ta tura karin jami’ai, ta tarwatsa su tare da kama mutane shida.
Read also: Sarah Palin Defends Trump, Criticizes Kamala Harris for ‘Lies’ & Media Bias
Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da bincike domin kamo sauran wadanda suka tsere.
Haka kuma, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya a jihar ba, tare da yin alkawarin cewa duk masu aikata daba za su fuskanci hukunci bisa doka.
